Saturday, 2 June 2018

Kace dai kawai kana jin tsoron yanda 'yan Najeriya suka gaji da mulkinka>>Martanin PDP, APGA ga shugaba Buhari da yace yana fargabar 'yan Adawa sunfi APC kudi

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana fargabarshi da irin kudin da 'yan adawa ke dasu a hannunsu wanda yace suna da isassun kudi da zasu kashe wajan shiryawa zaben shekarar 2019 wanda su APC basu da irin wadannan kudin.


Shugaba Buharin ya bayyana hakane lokacin da yake jawabi ga kungiyar magoya bayanshi da suka kaimai ziyara a fadarshi dake Abuja, ya kara da cewa 'yan adawar kuma suna amfani da kudin da suke dakwai wajan daukar nauyin tashe-tashen hankula a kasarnan dan batawa gwamnatinshi suna.

Ya godewa kungiyar magoya bayannashi bisa irin soyayyar da suka nuna mishi.

Saidai a martaninta, jam'iyyar PDP ta bayyana cewa, kawaidai Buharin yace yana jin tsoron yanda 'yan Najeriya suka gaji da shine kuma suke jiran zabe yazo su saukeshi.

Me magana da yawun PDP Kolu Olugbondian ya bayyana cewa, ba kudin dake hannun 'yan adawa ya kamata ya damu Buhari ba, abinda ya kamata ya dameshi shine irin yanda shekara daya kamin zaben 2019 'yan Najeriya sun nuna cewa sun gaji da mulkinshi saboda be cika musu alkawuran da ya daukar musu ba lokacin yakin neman zabe dan haka suke jiran zaben 2019 dan su saukeshi daga mulki.

Shima dan takarar shugabn kasa karkashin jam'iyyar PDP Kabiru Tanimu Turaki ya bayyana cewa babu ta yanda za'ayi ace jam'iyyar adawa tafi jam'iyya me mulki kudi, bai taba faruwa ba. Yace gwamnati tafi duk wani mutum da wata jam'iyya kudi, Ya kara da cewa kwanannan aka samu rahoton cewa gwamnati ta fitar da kudi dalar Amurka biliyan daya daga asusun rarar mai ba tare da amincewar majalisa ba, ana tsammanin kudin za'ayi amfani dasu ne wajan zaben 2019. Dan haka shugaban ya bamu wani labarin amma badai wannan ba.

Suma jam'iyyar APGA sun musanta wannan magana ta shugaban kasa inda sukace ba ta yanda za'ace wai jam'iyyar dake rike da fadar shugaban kasa da kuma madafin iko fiye dana jam'iyyun adawa ace jam'iyyun adawa sun fita kudi, me magana da yawun jam'iyyar Orji, ya bayyana cewa koda suna da kudi su ba siyasar kudi suke yi ba siyasar akida suke.
Vanguard.

No comments:

Post a Comment