Sunday, 10 June 2018

Kalli hotunan kwanannan na jarirannan da aka haifa a hade, likitoci suna rabasu a Yola

Wadannan hotunan 'yan biyun nanne da mukaji labarin an haifesu a hade amma kwararrun likitoci a cibiyar kula da lafiya ta gwamnatin tarayya dake jihar Adamawa suka rabasu, An saka musu suna Fatima da Maryam. An kuma sallamesu daga asibiti kuma kamar yanda ake iya gani a wadannan hotunan suna rayuwarsu cikin koshin lafiya.


Mahaifan yaran dai a wancan lokaci sun tabbatar da cewa kyauta aka musu aikin raba jariran. 

Muna fata Allah ya rayasu rayuwa me Albarka.No comments:

Post a Comment