Thursday, 28 June 2018

Kalli wasu matasa dauke da makamai suna biye da tawagar gwamna Ganduje na jihar Kano

Wadannan hotunan matasane a Ciromawa, karamar hukumar Garun Malam dake jihar Kano inda suke dauke da sanduna da adduna suna biye da gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje inda suke nuna goyon baya a gareshi.Gwamnan da ministan wuta, ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola da kuma kwamishinan 'yan sandan jihar, Rabiu Yusuf da sanata me wakiltar Kano ta kudu, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da sauran manyan ma'aikatan gwamnati sun halarci gurin kaddamar da fara aikin sake gina tagwayen titunan Kano zuwa Kaduna, Abuja wanda aka baiwa kamfanin Julius Berger kwangilar ginawa akan kudi naira biliyan 155.

Matasan dai sun fito ne dan nuna goyon baya ga gwamnan da tawagarshi.

Rahotanni sun bayyana cewa aikin titunan zai dauki tsawon watanni talatin da shida ana yinshi.

No comments:

Post a Comment