Monday, 11 June 2018

Kalli yanda akawa shugaba Buhari tarbar Karamci a kasar Morocco

A duk lokacin da shugaba Buhari ya kai ziyarar aiki jihohin Najeriya Dandazon jama'a sun sha yimai taron ban mamaki, musamman jihohin Arewa, hakanne ta faru a ziyarar da shugaba Buhari yakai kasar Morocco, jiya, inda akamai tarbar karamci.Sarki Muhammad VI na Moroccon da shugaba Buhari sun fito ta saman mota suna dagawa dandazon jama'ar da suka fito dan yiwa shugaba Buharin maraba, yayin da jami'an tsaro da jerin gwanon motocin alfarma ke kewaye dasu hagu da dama.Abin ya kayatar sosai, muna fatan Allah ya dawo dashi lafiya.

No comments:

Post a Comment