Saturday, 9 June 2018

Karanta amsar da Muhammad Salah ya baiwa Ramos akan ciwon da ya ji mishi

A karin farko tun bayan da yaji ciwo sanadin taho mu gama da sukayi shi da Ramos, Mohammed Salah yayi magana akan raunin nashi da yaji sannan kuma ya mayar da martani akan maganar da Ramos yayi.


Salah ya bayyanawa manema labarai cewa ya samu sauki sosai kuma yana fata idan yaji jikin nashi ya kara yin karfi, zai iya buga wasan farko da kasarshi zata buga da kasar Uruguay a gasar cin kofin Duniya da za'a buga a Rasha.

An tambayeshi shin ciwon da kaji shine ciwo mafi muni a tarihin wasan kwallo da kakeyi?

Sai ya bayyana cewa Eh tabbas hakane.

Da aka tambayeshi me zaice akan maganar da Ramos yayi ta cewa, shine ya fara kama hannunshi kuma Salah din ta bangare daban ya fadi sannan ta dayan bangren ne yaji ciwo.

Sai kawai Salah din ya fashe da dariya.

An tambayi Salah kuma me zaice akan maganar da Ramos yayi ta cewa da an mai allura zai iya dawowa ya ci gaba da buga wasan bayan hutun rabin lokaci,

Sai Salah ya sake yin dariya yace, nikance babu damuwa idan mutumin da ya saka kuka ya zama mutum na farko da zai saka dariya, da yayi kokari kuma ya gayamin cewa ko zan iya buga wasan gasar cin kofin Duniya.

An kuma tambayi Salah shin Ramos ya aike mishi da sako?,

Sai yace, Eh ya aikomin da sako amma ban gayamai cewa babu matsalaba.
Kamar yanda Marca ta ruwaito.

Ramos dai ya bayyana a wata hira da akayi dashi cewa ya aikewa da Salah sako kuma ya gayamai cewa yana samun sauki, babu matsala.

No comments:

Post a Comment