Sunday, 3 June 2018

Karanta labarin bahaushiyar da ta hadu da bature ta musuluntar dashi kuma suka yi aure

Tun bayan da labarin baiwar Allannan da ta fito daga garin Kano wadda wani baturen kasar Amurka ya biyota har Najeriya aka daura musu aure ya bayyana, sai wasu sauran labaran yanda matan arewa suka auri turawa suka rika bayyana.


Wannan baiwar Allahn wadda hotonta ke sama ta bayyana cewa ta gamu da baturenne a gurin shakatawa na Yankari inda daga nan suka fara magana, kwatsam rannan sai gashi a gidansu rike da Qur'ani  a hannunshi, ta tambayeshi me yake yi dashi yace karantawa yake, kuma idandai ta yarda zata aureshi zai musulunta.

Haka kuwa akayi, ya mulunta suka yi aure tun shekarar 1998, shekaru 20 kenan, tace har sun samu 'ya'ya tare.
Muna fatan Allah ya sanya Albarka a wannan iyali.
Itama wannan baiwar Allahn ta bayyana cewa aurenta biyu kuma tana da 'ya'ya haka ta hadu da wannan baturen wanda musulmine, suka yi aure, tace kusan shekararsu uku kenan yanzu da yin aure. Muna fatan Allah ya sanya Alheri.

Northernhibiscus.

No comments:

Post a Comment