Wednesday, 20 June 2018

Karanta yanda wani mutum ya dawo gida yayin da ake tsaka da shirin saka gawarshi kabari

A kauyen Santa Teresa dake kasar Paraguay wani lamari ya faru daya dauki hankulan mutane, wani matashine dan kimanin shekaru ashirin da aka fidda tsamani dashi,iyalanshi suka fara shirin yimai jana'iya har an dauki akwatin gawarshi za'a kai kabari sai gashi ya shigo gida.


Jaridar Mirror ta kasar Ingila ta ruwaito cewa matashin me suna Juan Ramon Alfonso ya bacene kwana da kwanaki har danginshi suka cire rai dashi, bacewar tashi ta zo daidai da fadan da wasu dilolin kwaya sukayi, kuma sai 'yan sanda suka tsinci gawar wani wanda aka kasa gane ko wanene.

Iyalan Juan sunyi amannar cewa wannan gawar dan uwansu ce dan haka kawai suka kama shirin binneta, aikuwa ana tsaka da wannan shiri sai gashi ya shigo gida.

No comments:

Post a Comment