Thursday, 14 June 2018

Karanta yanda wannan mutumin ya dafa kafarshi ya ba abokanshi suka ci

Wani labari daya dauki hankulan Duniya a wannan satin shine na wani mutum daya dafawa abokanshi kafarshi da aka yanke ya kuma basu suka ci a matsayin nama ba tare da saninsu ba.


Lamarin ya farune kusan shekaru biyu da suka gabata, bayan da rashin lafiya ta samu mutumin, likitoci suka yankemai kafar. Ya bukaci a abashi kafarshin da aka yanke ya tafi da ita gida, kuma haka akayi bayan daya cika sharuddan da ake bukata.

Mutumin yace yayi tunanin daskarar da kafar domin yin wani amfani da ita, kamar makarin kofa ko gurin ajiye fitila amma sai baiyi hakan ba.

Ya gayyanci abokanshi inda ya shirya musu liyafar cin abinci ya kuma dafa kafar tashi ya basu ita suka sha lagwada.

Mutumin ya bayyana wannan labarine a shafin sada zumunta na Reddit, tun bayan daya wallafa wannan labari hankulan mutane musamman ma'aboka shafukan yanar gizo ya karkata kanshi inda akaita bayyana ra'ayoyi kala-kala.

No comments:

Post a Comment