Sunday, 24 June 2018

Kasar Saudiyya ta hana 'yan kasar Qatar zuwa Umrah da Hajji

Qatar: Saudiyya da kawayenta sun hana mu zuwa Umra da Hajji
Shugabannin Qatar sun sanar da cewa, duk da Saudiyya da kawayenta sun nuna cewa babu wata masatala,suna ci gaba da yi ma ta bita-da-kulli,inda suke hana al'umarsu zuwa umra da Hajji.


Shugaban hukumar kare hakkin bil adama ta kasar Qatar,Ali bin Smaikh El-Merri wanda shi ne ya furta wannan kalamin,ya yi tsokaci kan alakar da ke tsakanin kasarsa da Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da kuma Masar.

Shekara daya kenan da wadannan kasashen suka dauki matakin kakaba wa Qatar takunkumi tare yanke duk wata lakar diflomasiyya da ke tsakanin su a watan Yunin shekarar 2017.

El Merri wanda ya ce Saudiyya da kawayenta suka gabatar da hujjojin karya kan ta ya ce:

"Shekara daya kenan da wadannan kasashen suka saka mana takunkumi.Babu abinda ya samu hukumominmu.Haka zalika tattalin zarzikinmu ma na ci gaba da bunkasa.Yanke alakarsu da mu, bai yi wani tasiri ba.Amma idan muka kalli ta fuskar mutane da kuma hakkokinsu, ko shakka ana iya cewa akwai babban zalunci.Saboda takunkumin ya girgiza gimshikan zamantakewar al'uma".

Daga karshe ya ce,
"Don ganin al'umarsu sun je kasa mai tsarki don sauke farali,mun gabatar wani rahoto na musamman  a hukumar kare hakkokin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya.Saboda har yanzu na ci gaba da yi mana zagon kasa a wannan fannin".
trthausa.

No comments:

Post a Comment