Tuesday, 12 June 2018

Kayan da Super Eagles suka saka zuwa kasar Rasha sune mafiya kyau tsakanin kasashen Duniya

Tawagar 'yan kwallon kafar Najeriya, Super Eagles sun samu yabon kasancewa wanda suka kaya mafi kyau da kayatarwa zuwa kasar Rasha tsakanin kasashen Duniya da zasu buga gasar cin kofin Duniya.Kafar labarai ta BBC ce ta bayyana haka yayin da ake saura kwanaki biyu a fara gasar,kamar yanda kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN ya ruwaito.


Kwanaki kadan da suka gabata wata mujallar kwalliya ta Duniya me suna GQ ta bayyana cewa kayan 'yan kwallon Najeriyar sune mafiya kyau tsakanin kasashen Duniya.

Muna fatan yanda kaya sukayi kyau Allah yasa wasama yayi kyau.

No comments:

Post a Comment