Saturday, 9 June 2018

Koda bamu samu nasara a gasar cin kofin Duniya ba to zamu zama wanda suka je da kayan da suka fi na kowace kasa kyau>>John Boyega

Tauraron fina-finan Amurka wanda yayi suna a cikin fim din Star Wars, kuma dan asalin Najeriya, John Boyega kenan sanye sa rigar 'yan kwallon Najeriya, ya bayyana cewa,duk da dai ya makara amma gata shima ya saka.


Ya kara da cewa idan ya saka rigar sai ya zama me cin Amala, sannan kuma saka rigar kanshi yana kara bashi karfin gwiwa akan 'yan kwallon na Najeriya.

Ya kara da cewa koda ma dai bamu samu nasara ba a gasar cin kofin Duniyar, zamu zama wanda suka je da kayan da suka fi na kowa kyau a bana.

No comments:

Post a Comment