Saturday, 30 June 2018

Kofin Duniya: Faransa ta kora Argentina gida


Faransa ta fitar da Argentina daga gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Rasha.
Kwallaye bakwai aka ci a wasan, inda Faransa ta doke Argentina 4-3.Griezmann ne ya fara cin Argentina ana minti 13 da wasa a fanareti, Angel Di Maria kuma ya farke kwallon ana minti 41.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci Mercado ya ci wa Argentina kwallo ta biyu ana minti 48 da wasa amma Pavard ya farke wa Faransa kwallo a minti na 57.

Mbappé ne ya ci wa Faransa kwallaye biyu a minti na 64 da 68. Sai bayan an kara lokaci ana dab da hure wasa Agüero ya ci wa Argentina kwallo ta uku.

Yanzu an fitar da Argentina da Jamus da suka buga wasan karshe a Brazil 2014. Kuma an fitar da su ne a Kazan Arena, filin da Koriya ta kudu ta yi waje da Jamus kasar da ke rike da kofin gasar.


Hakan dai ya tabbatar da kofin duniya ya gagari Messi wanda babu abin da bai ci ba a Barcelona.

Zai iya kasancewa wannan ce gasar cin kofin duniya ta karshe ga Messi.
Da kyar Argentina ta tsallake zuwa zagaye na biyu daga rukunin D bayan ta samu sa'ar Najeriya ci 2-1.

Tun kafin haduwar Faransa da Argentina ake ganin yadda tawagar Messi ta Argentina suka sha wahala a wasannin rukuni yana da wahala su iya doke Faransa.


Bayan ficewar Messi daga Rasha yanzu ido zai koma kan makomar Ronaldo a gasar cin kofin duniya.

Cristiano Ronaldo wanda ya lashe kofin zakarun turai sau uku a jere yana fatan jagorantar Portugal ga nasarar tsallakewa zuwa zagayen kusa da dab da karshe a karon farko tun 2006.

Ronaldo na Portugal da ya lashe kofin Turai a 2016, zai fafata ne da tawagar su Luiz Suarez ta Uruguay.

Uruguay dai tana cikin sahun kasashe uku da suka tsallake zuwa zagaye na biyu ba tare da an doke su ba, da suka hada da Croatia da kuma Belgium.

Messi da Ronaldo sun lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya a shekaru 10 a tsakaninsu.
Yanzu wata dama ce ga Ronaldo bayan an yi waje da Messi a gasar cin kofin duniya.
bbchausa


No comments:

Post a Comment