Saturday, 16 June 2018

Kotu ta daure Cristiano Ronaldo shekaru 2 a gidan yari

Wata kotun kasar Andalus ta yanke wa fittacen dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo hukuncin zaman gidan yari na shekaru biyu saboda kauracewa biyan haraji da gangan.


Sai dai an ruwaito cewa Ronaldo ya nemi sassauci inda ya ke bukatar a janye hukuncin zuwa gidan yarin  a sa mishi diyya ya biya maimakon zaman gidan yarin.

Ronaldo dai zai biya kudin harajin da ake binshi har miliyan 18.8, sannan kuma zaije gidan yari na tsawon shekaru biyu kamar yanda hukuncin kotun ya bayyana, haka kuma a kwai sauran wani hukunci guda da ba'a bayyana ba a akan Ronaldon wanda zai iya zama hukuncin babban laifi dalilin rashin biyan harajin.

Ronaldo dai ya amince da hukuncin kotun inda yanzu yake neman sassauci akanshi sannan yana daridarin wane hukunci kotu zata yanke a dayar shari'ari.

No comments:

Post a Comment