Thursday, 28 June 2018

Kotu ta wanke Tsohon Gwamna Sule Lamido

Wata babbar kotun jiha a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, ta wanke tsohon gwamnan jihar tare da sallamarsa daga tuhume-tuhumen da gwamnatin jihar ta ke yi masa.


A bara ne aka tuhumi Sule Lamido da laifin tunzura magoya bayansa, da yunkurin ta da zaune-tsaye da kuma bata suna gabanin zaben kananan hukumomi a gaban wata kotun majistiri.

Masu shigar da kara sun ce tsohon gwamnan ya yi kalaman ne a lokacin wani gangamin siyasa a jihar ta Jigawa.

Tun da farko lauyan wanda ake kara, Yakubu Ruba, ya kalubalanci hurumin kotun na saurarar karar yana mai cewa ba a bi tsarin doka ba wurin gabatar da karar.

Amma kotun, wacce Mai Shari'a Usman Mohammed Lamin ya ke jagoranta, ta yi watsi da bukatar lauyan tana mai cewa babu wata ka'ida da aka sabawa, abin da ya sa shari'ar ta ci gaba da gudana.

Sai dai ana cikin shari'ar ne lauya Yakubu Ruba ya daukaka kara zuwa babbar kotun jihar kan hujjojin da ya bayar tun farko, inda ya nemi kotun majistirin da ta tsayar da shari'ar har sai abin da hali ya yi.

A hukuncin da suka yanke a ranar Laraba, masu Shari'a Ahmed Musa Gumel, da Umar Sadiq da Abdulhadi Suleman na babbar kotun jihar, sun sallami tsohon gwamnan, sannan suka yi watsi da duk tuhumar da ake yi masa kamar yadda lauyansa ya bukata tun farko.

Tun lokacin da aka shigar da shari'ar dai, tsohon gwamna Lamido da magoya bayansa suka yi watsi da zarge-zargen suna masu cewa siyasa ce kawai.

Kafar yada labarai ta Premium Times ta rawaito mai magana da yawun gwamnan jihar na yanzu Bello Zaki, yana cewa gwamnatin jihar ba za ta daukaka kara kan hukuncin ba.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment