Sunday, 10 June 2018

Kungiyar kwallon kafar Egypt sun isa Rasha tare da Mohammed Salah

Tawagar 'yan kwallon kasar Misra/Egypt sun isa kasar Rasha a jiya, Asabar inda zasu shiga gasar cin kofin zakarun turai da za'a yi, anga tauraron kwallon kasar, Muhammad Salah cikin wadanda suka isa Rashar.


Salah dai ya nuna alamar jin sauki sosai daga ciwon daya samu a wasan karshe na cin gasar kofin zakarun turai wanda suka yi taho mu gama shi da Ramos.
Ko da a atisayen karshe da kungiyar kwallon Egypt din sukayi, an ga Salah, saidai be shiga an motsa jikin dashi ba, yadai dagawa masoyan sa hannu, kamar yanda jaridar Independent ta ruwaito.

Ranar Juma'a idan Allah ya kaimu Egypt din zata buga wasan farko da kasar Uruguay.

No comments:

Post a Comment