Saturday, 23 June 2018

Kwallaye Biyun Da Ahmed Musa Ya Ci Abin Alfahri Ne Ga Al'ummar Arewacin Nijeriya, Cewar Abdullahi Shehu

Mai tsaron bayan Super Eagles ta Nijeriya, Abdullahi Shehu ya yi matukar nuna farin cikin sa game da kwallaye biyun da amininsa Ahmed Musa ya zura a wasan Nijeriya da Iceland a gasar cin kofin duniya na 2018 da aka buga yammacin yau Juma'a.


Abdullahi Shehu, wanda ya bayyana hakan a yayin tattaunawarsa da RARIYA ta waya, ya kara da cewa kasancewar wasa ne wanda daukacin al'ummar Nijeriya suke kallo, hakan ya sanya kwallaye biyun da Ahmed Musa ya ci ya sanya su alfahari, musamman al'ummar Arewacin Nijeriya, wato yankin da dan wasan ya fito.

Shehu ya ci gaba da cewa wani abin farin ciki kuma shine, ko a wasan da Nijeriya ta buga da Ajantina a gasar cin kofin duniya da ta gabata, Ahmed Musa ne ya ci kwallaye biyu kuma ga shi ya sake maimaitawa.

Shehu ya kuma yi kira ga 'yan Nijeriya da su ci gaba da mara musu baya tare da yi musu addu'a don ganim sun ci gaba da samun nasara a gasar.
rariya.

No comments:

Post a Comment