Saturday, 9 June 2018

Lai Muhammad ya bijirewa umarnina ya mayarwa da Obasanjo martani>>Shugaba Buhari

A lokacin da kungiyar magoya bayanshi suka kaimai ziyara a fadarshi dake babban birnin tarayya, Abuja, jiya Juma'a, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gode musu da wannan ziyara sannan ya bayar da labarin yanda ministan watsa labaranshi ya bijirewa umarninshi wajan mayarwa da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo martani.


Shugaba Buhari yace lokacin da Obasanjo yai magana, me magana da yawunshi, Femi Adesina ya yunkuro da kokarin mayar mishi da martani amma sai ya hanashi saboda abubuwa biyu, Buhari yace abu na farko da ya sa ya hana Adesina mayarwa da Obasanjo martani shine, Adesinan yaro ne, ba sa'ansu bane.

Sannan kuma Buharin da Obasanjon sun fito daga bangare dayane a gidan soja.

Buhari ya kara da cewa amma fa da ministan watsa labarai, Lai  Muhammad yazo yace mai saiya mayarwa da Obasanjo martani, yace mai a'a, amma Lai Muhammad ya nace akan cewa ya barshi ya mayarmai da martani, sai Buharin yace to me zaka gaya mishi?

Lai Muhammad ya mai bayanin cewa zan gayawa 'yan Najeriya yanda muka iske gwamnati da abinda mukayi da kuma matsayin da muke ciki a yanzu, daga nanne sai ya kyaleshi ya mayarwa da Obasanjon martani.

Shugaba Buhari yace kuma Lai Muhammad din yayi kokari a martanin da ya mayarwa da Obasanjon, domin mutane da dama sun kirashi suka gayamai cewa Lai Muhammad din yayi kokari sosai

No comments:

Post a Comment