Saturday, 30 June 2018

Laurent Simons zai fara karatun jami'a yana dan shekara 8

Wani yaro a kasar Belgium zai fara karatun jami'a yana da shekara takwas bayan ya kammala karatunsa na sakandare.


Laurent Simons, ya samu shedar kammala karatun sakandare da ake yi tsawon shekara shida amma cikin shekara daya da rabi.

Iyayen yaron sun ce an auna kaifin basirarsa inda kuma ya bada mamaki ya samu babban makin da ake bukatar dalibi ya samu.

Laurent ya karbi takardar difloma tare da abokan karatunsa 'yan shekara 18.

A lokacin da yake zantawa da wata kafar yada labarai ta Belgium, Laurent ya ce ya fi son darasin lissafi saboda fadinsa domin ya kunshi darussa da suka kunshi ilimin kididdiga da algebra.

Bayan ya kammala hutun wata biyu, Laurent zai soma karatun jami'a.

Mahaifinsa ya ce lokacin da dansa yana karami ya yi fama wajen wasa tare da wasu yara, kuma shi yaro ne da ba ya sha'awar kayan wasan yara.

Yaron ya ce da farko ya fi son ya zama likitan tiyata ko kuma dan sama jannati amma yanzu yana tunanin ko zai karanci ilimin kwamfuta.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment