Saturday, 2 June 2018

Lokacin ina PDP mun rika kashe mutanen gari da abokan hamayya dan samun nasarar zabe>>Inji Tsohon gwamnan Abia

Orji Uzor-Kalu
A taron da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC yankin Kudu masu gabas suka gudanar a Abuja, tsohon gwamnan  jihar Abia, Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa a lokacin yana PDP sukan kashe mutanen gari da abokan hamayyarsu dan su samu nasara.Yana bayanine akan zaben shuwagabannin jam'iyyar da aka gudanar kwanannan cikin kwanciyar hankali inda yace, ada a da lokacin ina PDP abubuwa da yawa na faruwa, idan akace za'ayi zabe irin wannan, mukan kashe abokan hamayya haddama jama'ar gari dan kokarin samun nasara wanda hakan be dace ba.

Wannan magana tashi ta dauki hankulan 'yan Najeriya sosai inda akayi ta mayar da zafafan martani akanta, shidai Kalu yayi gwamna na tsawon wa'adi biyu a jam'iyyar PDP, daga baya kuka ya koma jam'iyyar APC.

Saidai jam'iyar PDP ta nisanta kanta da wannan kalami nashi inda ta fito tace batasan wannan magana da Kalu yayi ba, ita bata taba bayar da umarnin kashe wani ba, jam'iyyace me bin doka da oda wadda kuma aka kafata bisa tsari me kyau.

Sun kara da cewa watakila Kalu yana magana akan dabi'arshice shi kadai amma ba jam'iyyar PDP ba, sun kuma ce ya kamata ya fito ya gayawa 'yan Najeriya cikakken bayanin ikirarin da yayi kuma ya fadi su waye sauran da suke aikata wancan aiki tare dashi, kamar yanda Premium times ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment