Thursday, 21 June 2018

Makarfi ya dauki alwashin kawar da Buhari daga kujerar shugaban kasa

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, tsohon Sanata, kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na riko, Ahmed Muhammad Makarfi ya ziyarar motsa jam’iyyarsa ta PDP a garin Jos na jihar Filato, inda ya dau alwashin hambarar da gwamnatin shugaban kasa Muhamamdu Buhari. 


Makarfi ya bayyana haka ne a yayin dayake mika kokon bara ga uwar jam’iyyar PDP reshen jihar Filato, inda ya nemi da su bashi goyon baya a kokarinsa na zama dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, inji rahoton jaridar Sahara Reporters. 

Makarfi yana bugun kirji yana cewa muddin jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar shugaban kasa, tabbas ba zai sha wata wahala ba wajen baiwa shugaba Buhari kashi a zabukan da zasu fafata. 

Bugu da kari, Makarfi yace idan ya lashe zaben shugaban kasa zai kawo dawwamammen zaman lafiya, ba tare da siyasantar da lamarin a Najeriya ba, sa’annan yace zai dinga shawara da shugabannin al’umma da kuma shuwagabannin addinai. 

Dayake jawabinsa, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Filato, Damishi Sango ya bayyana cewa kafatanin yayan jam’iyayr PDP na jihar Filato suna tare da Makarfi dari bisa dari, musamman saboda yadda ya ceto PDP daga hannun tsohon shugabanta Ali Modu Sheriff.

 “Ba zamu taba mantawa da yadda Makarfi ya ceto jam’iyyarmu daga hannun Ali Modu Sheriff da yan barandansa ba, bayan doguwar gwagwarmaya da aka sha. Don haka muke son mutane irinsu Makarfi ya kwato Najeriya daga hannun Buhari, kamar yadda ya kwato PDP daga hannun Sheriff.” Inji shi. 

Dukkanin shuwagabannin jam’aiyyar PDP na kananan hukumomi goma sha bakwai sun halarci taron, haka zalika tsohon shugaban jam’yyar, Dukum Shun, inda shugaban PDP na jihar Kaduna, Hassan Hyet da sauran yayan jam’iyyar suka raka Makarfi zuwa Jos.

No comments:

Post a Comment