Saturday, 9 June 2018

Marar gaskiya ko a ruwa gumi yake>>Lai Mohammed ya mayarwa da Obasanjo martani

Buhari da Obasanjo
Gwamnatin Buhari ta ce aikin gyaran barnar da PDP ta yi ne ta sa a gaba, ba zargin da ba shi da tushe ba. A cikin sanarwar da ya fitar domin mayar da martani bayan Obasanjo ya zargi gwamnatin Buhari da kokarin kame shi, Ministan watsa labarai Lai Mohammed ya ce gwamnatinsu ba za ta bata lokacinta ba domin kokarin tozarta wani ba, ko kuma damuwa da wani zargin da ba shi da tushe.


A ranar Juma'a ne tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya fitar da sanarwa yana zargin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da kokarin kama shi.
Mista Obasanjo ya ce gwanatin Buhari na tattara shaidun boge domin ta daure shi saboda sukar da yake wa shugaban, inda ya ce rayuwarsa na cikin hatsari domin an kwarmata ma sa cewa yana cikin jerin sunayen mutanen da ake farauta.
A martanin da ya mayar, Lai Mohammed ya ce "gwamnatin Buhari ba za ta damu da wasu zarge-zargen da ba su da ma'ana ba, daga ko wane bangare da nufin karkatar da hankalinta ga ayyukan da ta ke."
Ya kara da cewa: "wadanda ke da kashi a jiki ne ya kamata su ji tsoro, marar laifi ba zai damu da wani bincike ba, a zahiri ko a mafarki".
"Hankalin gwamnati ya karkata ne ga kokarin gyara barnar da PDP ta yi a shekaru 16 kamar yadda ta fi mayar da hankali ga ci gaba da gina nasarorin da ta samu a shekaru uku"
"Wannan gwamnatin ba za taba karkata ga tozarta 'yan kasa marar laifi ba, wannan ba tsarin shugaba Buhari ba ne da kuma gwamnatinsa. Masu laifi ne kawai za su damu," in ji Lai Mohammed.
Ministan ya kuma ce gwamnatinsu na mutunta tsarin mulkin dimokradiya da 'yancin albarkacin baki, amma sun fahimci cewa wadanda a lokacinsu suka yi watsi da dokokin to zai ma su wahala.
Takun saka ya zafafa tsakanin shugabannin biyu tun bayan da Mista Obasanjo, wanda ya goyi bayan Buhari a zaben 2015, ya yi Allah-wadai da yadda yake gudanar da mulki, sannan ya ce bai cancanci a sake zabarsa ba a zaben 2019.
A 'yan kwanaki ne shi kuma Buhari ya zargi gwamnatin Obasanjo, wanda ya mulki kasar a matsayin zababben shugaba daga 1999 zuwa 2007, da "kashe dubban daloli kan wutar lantarki ba tare da an ga wutar a kasa ba". Obasanjo ya musanta wannan zargi.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment