Wednesday, 27 June 2018

Marcos Rojo ya bayyana sirrin da Messi ya gayamai da ya karfafa mishi gwiwa yaci Najeriya

Dan kwallon kasar Argentina daya ci Najeriya kwallo ta biyu da ta baiwa kasarshi damar samun nasara a wasan da aka buga jiya, Marcos Rojo ya bayyana abinda Messi ya gaya mishi daya bashi karfin gwiwar cin kwallon.


Rojo ya gayawa manema labarai bayan kammala wasan cewa, bayan da aka dawo hutun rabin lokaci kuma Najeriya ta rama kwallon da suka ci ta, hankalinsu ya tashi duk suka rude, saura kadan da sun karaya amma sai Messi ya samesu yace kada su sakawa kansu damuwa da yawa.

Abinda yake so dasu shine dukansu hadda masu tsaron baya duk su fita kowa ya nemi cin kwallo, haka kuwa akayi ya samu yaci kwallonshi, Rojo yace Messi shine kaftin mafi kwarewa a Duniya, ya basu dabara kuma sunyi amfani da ita duk da cewa akwai hadari a ciki amma sun samu nasara.

No comments:

Post a Comment