Thursday, 14 June 2018

Marigayiyya Hauwa Maina ta samu jika

Masha Allah! Fitacciyar jaruma kuma furodusa Hauwa Maina, wadda Allah ya yi wa rasuwa a ranar 2 ga Mayu, 2018, ta samu jika, domin kuwa diyar ta Maryam ta haihu a jiya.Da ma mujallar Fim ta ruwaito a lokacin da ake jimamin rasuwar Hauwa cewar Maryam Bukar Hassan ta na dauke da tsohon ciki.

Maryam ta haihu a Ranar Talata, 12 ga Yuni, 2018 a garin Kaduna, kuma ta samu da namiji lafiyayye. 

Wata kwakkwarar majiya ta shaida wa wakilin mu cewa ita ma maijegon lafiyar ta sumul.

Tun lokacin da ta baro Abuja inda ta ke aure ta zo Kaduna domin karbar gaisuwar rasuwar mahaifiyar ta, Maryam ta ci gaba da zama a gidan kakar ta (mahaifiyar Hauwa), ta na goyon ciki.

Ana sa ran za ta ci gaba da zama a Kaduna har zuwa lokacin da za ta yi arba'in, kafin ta koma gidan mijin ta, Umar Ahmed Zuruq, a Abuja.

A wani sako da ta rubuta a shafin ta na Instagram, Maryam ta bayyana farin cikin samun wannan k'aruwa da ta yi. Ta ce kakar yaron ta so ta yi tozali da jikan nata, to amma Allah bai kaddara hakan ba. 

Ta bayyana wannan haihuwa a matsayin wani babban abin farin ciki da ya same ta a daidai lokacin da ta ke cikin jin zafin rabuwa da mahaifiyar ta. 

Mu na addu'ar Allah ya raya abin da aka samu, ya ba Maryam cikakkiyar lafiya, kuma ya jikan Hauwa Maina, amin.
Fimmagazine.

No comments:

Post a Comment