Saturday, 30 June 2018

Mascherano ya ajiya bugawa kasarshi ta Argentina kwallo bayan da suka sha kashi a hannun Faransa: Ya kafa tarihin zama dan wasan da yafi yawan jan kati a gasar cin kofin Duniya

Bayan fitar dasu da Faransa tayi daga gasar cin kofin Duniya, tauraron kwallon kafar kasar Argentina, Javier Mascherano ya bayyana cewa ya ajiye bugawa kasar tashi kwallo, yace sunyi iya bakin kokarinsu amma nasara ba'a hannunsu take ba.


Ya bayyanawa 'yan jaridu cewa zai koma me goyon bayan kungiyar kwallon kafar kasar tashi kuma yana fata wataran su yi abinda su suka kasa yi yau.

Saidai a wasan na yau Mascherano ya samu katin gargadi wanda da ace sun wuce zuwa wasan kusa da na kusa dana karshe to da bazai buga wasan ba saboda dama yan da katin gargadin watau, Yellow Card, da aka bashi a wasan da suka buga da Najeriya.

Wannan kati na bakwai kenan da Mscherano ya samu a gasar cin kofin Duniya wanda yasa ya zama dan wasa na daya a Duniya da yafi yawan jan kati a gasar, kamin Mascherano, Zidane ne na daya da yawan jan kati shida.

No comments:

Post a Comment