Tuesday, 12 June 2018

Masu laifin da suka gogawa Dino Melaye cewa shi ke basu makamai yanzu sun musanta hakan

Sanata Dino Melaye da masu laifin da aka kama bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, Kabiru Saidu da Nuhu Salisu wanda sukace Sanata Melaye ne ke basu makamai duk sun musanta wannan zargi da ake musu.


Wadanda ke zargin sun musanta cewa sanata Melaye ya basu bindiga sannan kuma sun musanta laifin da ake zarginsu dashi, haka shima Dino ya musanta hakan a gaban kotun Magistre ta jihar Kogi da aka gurfanar dasu jiya Litinin.

Lauyan Dino Melaye yace wannan laifine babba dake bukatar a gabatar da shaidu da zasu bayar da ba'asi a gaban kotu.

Alkali Sulaiman Abdullahi ya daga sauraron karar zuwa 26 ga watan gobe inda ya bayyana cewa yana so a gama shari'ar cikin hanzari.
Dailytrust.

No comments:

Post a Comment