Wednesday, 13 June 2018

Matashi yayi nadamar mayar da kudi 50000 daya tsinga ga mai su bayan da ya bashi ladar 2000

Wani ɗan Najeriya mai suna Ifeanyi da ya tsinci kuɗin wani mutum da yayi siyayya a shagonsa har Naira 500,000 ya bayyana rashin jin daɗinsa ƙarara game da yadda mai kuɗin ya ba shi Naira dubu biyu kacal.

Ifeanyi dai ya wallafa a shafin sadarwarsa na Twitter domin bayyana irin abinda ya kira kwauro, a cewarsa duba da yawan kuɗin da kuma cewar shi mai kuɗin ya manta inda ya ajiye su, kamata yayi a ce ya ba shi abinda yafi haka.

Ya bayyana cewa, a lokacin da mutumin ya dawo yana cigiyar ko ya bar kuɗin a shagonsa, sai na ɗagn tsokane shi na ce masa ban gani ba, kawai sai na ga ya juya zai tafi, daga nan ne na kira shi na miƙa masa kuɗinsa.

Sai da ya rungume ni don tsananin murna, amma wai ga mamaki na sai naga ya ba ni dubu biyu kacal.

Wannan jawabin da Ifeanyi yayi a shafin nasa na Twitter ya sanya mutane mayar masa da martani, inda wasu suke cewa da ma ba don Allah ya bayar ba wasu kuma suke cewa tunda ba nasa ba ne ai bai kamata ya damu ba.

No comments:

Post a Comment