Thursday, 28 June 2018

"Messi zai yi bankwana da Argentina"

Labarin ficewar Messi daga kungiyar kwallon kafar Argentina ya gama duniya,inda a yanzu haka ya haifar da zazzafan cece-kuce.


Labarin dai na ci gaba yaduwa duk da Argentina ta karyata batun.

Bayan da Argentina ta lallasa Najeriya 2 da 1 kuma, sai lamarin ya yi tsamari.

An tabbatar da cewa shahararren dan wasan na gaf da yin bakwana da Argentina a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018.

Tauraron wasan kwallon kafa Messi ya fito fili don yi tsokaci kan wannan lamarin inda ya ce,

"Ina ci gaba da mafarkin mun daga kofin duniya sama.Ina da tabbacin karfin wannan fatan da ya lullube zuciyata.Ba zai yiwu ba in juya wa wannan fatan baya ba a sauwake.Na lashe dukannin muhimman kofi,amma bana zaton zan juya wa Argentina baya ba tare da ta lashe kofin duniya ba".

A wasan da za a buga a nan gaba, Argentina wacce ke a sahu na 2 a jerin kungiyoyin wasanni na rukunin D, za ta kara da Faransa zakara a rukunin C.
Trthausa.

No comments:

Post a Comment