Friday, 29 June 2018

'Messin Iran' ya yi ritaya saboda an 'zagi' babarsa

Dan wasan gaba na Iran Sardar Azmoun ya yi ritaya daga buga wa kasar kwallo yana mai shekara 23, bayan ya yi zargin cewa mahaifiyarsa ta kamu da rashin lafiya saboda zagin da aka rinka yi mata.


Azmoun - wanda ake wa lakabi da "Messin Iran" - ya ci wa kasar kwallo 23 a wasa 33 kafin gasar.

Amma bai ci ko daya ba a gasar ta Rasha a inda tawagar ta Carlos Queiroz ta kare a mataki na uku bayan Spain da Portugal.

Azmoun ya bayyana matakin da ya dauka na daina buga wa kasar kwallo da cewa "abin damuwa".

Ya ci kwallo 11 a wasa 14 na share fage, kuma ya buga minti 90 a dukkan wasanni uku da kasar ta buga.

Sai dai Azmoun ya ce kushe shi da aka rinka yi ya sa mahaifiyarsa rashin lafiya.

"Mahaifiyata ta warke daga mummunar cuta kuma na yi farin ciki," a cewar Azmoun, wanda ke taka leda a kulob din Rubin Kazan na Rasha.

"Abin takaici shi ne zagi da cin mutuncin da wasu mutane suka rinka yi min da abokan wasa na, ya sa cutarta ta kara kamari.

Azmoun ya fara buga wa Iran kwallo tun yana dan shekara 19.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment