Wednesday, 13 June 2018

Mohamed Salah ya fara atisaye

Tauraron kwallon kafar kasar Egypt/Misra, Mohamed Salah ya fara atisaye tare da sauran 'yan kwallon kasar a kasar Rasha inda suke Shiryawa gasar cin kofin Duniya, Salah dai yana kara murmurewa daga ciwon da yaji a kafada sanadiyyar taho mu gama da yayi shida Ramos.Saidai masu kula da kungiyar ta kwallon kafar Egypt sun bayyana cewa, tabbas akwai alamun samun sauki sosai tare da Salah amma babu tabbacin zai buga wasan farko da kasar zata buga da kasar Uruguay ranar Juma'a.

Sunce dai suna nan suna kara kula da yanda yake kara murmurewa, kamar yanda SkySport ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment