Sunday, 3 June 2018

Mu saka jihar Zamfara cikin addu'a

Assalamu alaikum jama'a daya daga cikin masu bibiyar shafin hutudole.com daga jihar Zamfara me suna maman Hajara, tana rokon addu'a daga 'yan uwa musulmi akan rikice-rikicen dake faruwa a jihar, tayi rokon jama'a su saka su a addu'a Albarkacin wannan wata na Ramadana da muke ciki.

Muna fatan Allah ya kawo karshen wannan tashin hankali, 'yan uwa musulmai da suka rasa rayukansu a cikin rikicin Allah ya gafarta musu, da sauran jihohin dake fama da tashin tashina baki daya.

No comments:

Post a Comment