Thursday, 28 June 2018

Muma bamu ji dadi ba da aka fitar damu: Mun gode da goyon bayanku>>Sakon Ahmad Musa ga 'yan Najeriya

Tauraron dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya fitar da sakon godiya ga 'yan Najeriya bisa irin goyon bayan da suka nuna wa kungiyar su ta Super Eagles a gasar cin kofin Duniya da suka buga a kasar Rasha.Ya kuma gode da damar da ya samu ta wakiltar kasarshi a gasar cin kofin Duniya inda yayi goyayya da shahararru, yace duk da basu yi nasara ba amma sun yi iya bakin kokarinsu har zuwa karshen da aka fitar dasu,  yace kamar yanda kuke jin ba dadi muma, 'yan wasan munji ba dadi da aka fitar damu kuma zamu yi amfani da wannan ya zama mana karin karfin gwiwa dan komawa da kuzarin mu. Mu 'yan Najeriyane kuma ina fatan zamu ci gaba da sanyaku alfahiri.


No comments:

Post a Comment