Thursday, 14 June 2018

Nafisa Abdullahi zata bude shagon dinki

Yayin da ake shirin bukukuwan sallah karama, daya daga cikin abubuwan da akeyi da Sallah shine sabon dinki inda zakaga maza da mata, yara da manya duk ansha sabbin dinkuma, saidai Ba sabon abu bane irin yanda duk sallah ake samun rashin cika alkawarin dinki daga gurin mafi yawan teloli. Jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi dai tace daga wannan Sallar tela ya dena mata yangar dinki dan kuwa zata bude shagon dinkinta Hasalima tace an gama mata dinkunanta.

Nafisar tace ta shirya tsaf da bude shagon dinkin bayan sallah inda tuni ta tanadi teloli da duk wani abu da take bukata dan fara wannan sana'a.

Muna fatan Allah yasa a fara a sa'a.

No comments:

Post a Comment