Sunday, 3 June 2018

Najeriya zata dauki nauyin taron Majalisar dinkin Duniya

Ministan Labarai da al'adu na Najeriya, Alhaji Lai Muhammad, ya bayyana amincin sa dangane da shirye-shiryen da ake gudanarwa a kasar nan ta Najeriya domin daukar nauyin taron yawon buɗe ido da shakatawa na Majalisar 'Dinkin Duniya.


Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito, Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar kimanta harabar da za a gudanar da taron a farfajiyar Otel din Transcorp dake babban birnin Kasar nan Abuja.

A shekarar da ta gabata ne Najeriya ta samu damar daukar nauyin taron hukumar kula da harkokin yawon shakatawa na duniya da za a gudanar a ranar 4 zuwa 6 ga watan Yuni a garin Abuja.

Ministan yake cewa, ya yi matukar farin ciki da gamsuwa dangane da yadda Najeriya take ci gaba da gudanar da shirye-shiryen daukar nauyin taron majalisar dinkin duniya, inda ya kuma yabawa kwazon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Yake cewa, a sakamakon hobbasan shugaba Buhari na magance kalubalan tsaro a kasar ya sanya Najeriya ta samu damar daukar nauyin taron majalisar Dinkin Duniya da zai tabbatar wa da Duniya zaman lafiya da kwanciyar hankali da ya wanzu a cikin ta.

Ya kara da cewa, wannan shiri shi zai tabbatar da labarin cewa Najeriya a cikin shirin daukar nauyin duk wani taro na duniya a sakamakon nasarorin da gwamnatin shugaba Buhari ta yi na cin galaba akan ta'addanci.

Kamafanin Dillancin Labarai na Najeriya ya kuma ruwaito cewa, kimanin wakilai 180 daga kasashen ketare ne za su halarci taron kwanaki ukun da za a gudanar wanda zai hadar har da Ministoci 26 na yawon Shakatawa daga kasashen Afirka.

No comments:

Post a Comment