Thursday, 14 June 2018

Naji bakin cikin da rabon inji irinshi tun rasuwar mahaifita lokacin da Sifaniya suka koreni daga aiki>>Inji sabon kocin Real Madrid Julen Lopetegui

A lokacin da yake sa hannu a kan takardar alkawarin kama aikin horas da kungiyar Real Madrid a yau, Alhamis, Julen Lopetegui ya bayyana cewa lokacin da kasar Sifaniya ta bayyana cewa ta koreshi da ga aiki yaji bakin cikin da rabon da ya ji irinshi tun mutuwar mahaifiyarshi.


Amma yace wannan sabon aikin daya kama ya sakashi cikin farin ciki marar misaltuwa inda ya godewa me kungiyar Real Madrid, Florentino Perez da kuma daukacin kungiyar bisa yadda da sukayi da shi har suka bashi wannan aiki, yace burinshi shine samun nasara a duk wata gasa da zasu shiga.

Perez yace sun bayyana sanarwar daukar Lopetegui aikine kamin fara gasar cin kofin Duniya dan gujewa jita-jita ko kuma fitar labarin ta wata kafa a lokacin da ake tsaka da gasar cin kofin Duniya.

Kasar Sifaniya dai ta kori Lopetegui daga aikin horas da 'yan wasanta saboda bai sanar da ita shirin kama aikin horas da Real Madrid da yake ba.

No comments:

Post a Comment