Thursday, 21 June 2018

Ni ma dan Tijjaniyya ne>>Inji Shugaba Buhari

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shi fa na kowane dan Najeriya ne mai irin kowane addini, yare ko kabila ciki kuwa hadda Tijjaniyya tare da cewa shi babban burin sa shine na samar wa da 'yan kasa cigaba mai dorewa.

Shugaban yayi wannan ikirarin ne a fadar sa dake a Villa, jiya lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin darikar Tijjaniya a nahiyar Afrika karkashin jagorancin Sheikh Ahmed Tijjani Ibrahim Inyass dake zaman jika wurin Marigayi Sheikh Ibrahim Inyass.

Buhari ya godewa dukkan 'yan tijjaniyya dake a fadin duniya game da irin goyon bayan da suke nuna masa da kuma fahimtar manufofin sa na alheri da suke yi.

No comments:

Post a Comment