Thursday, 28 June 2018

PDP ta baiwa jama'ar jihar Filato shawarar kai shugaba Buhari kotin Duniya ta ICC dan bi musu hakkinsu kan kisan da akawa 'yan uwansu

Kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP (NWC) ya shawarci jama’ar jihar Filato da su maka shugaba Buhari a kotun shari’ar aikata laifukan aiyukan ta’addanci ta Duniya (ICC) saboda kisan kare dangi da aka yi a jihar na baya-bayan nan.


Kazalika ta bayyana cewar, ta shiga alhini na tsawon kwanaki bakwai (7) domin jajantawa jama’ar jihar iftila’in da ya afka masu.

A jawabin da jam’iyyar ta fitar ta bakin sakataren ta na yada labarai, Kola Ologbondiyan, PDP ta bukaci mutanen jihar Filato da hada kai da wasu kungiyoyin kare hakkin bil’adama domin neman hakkin ‘yan uwan su da aka kashe da kuma asarar dukiya da suka yi sakamakon rigingimu, a karkashin gwamnatin Buhari.

“Duk ran dan Najeriya yana da muhimmanci, a saboda haka hakki ne a kan gwamnati ta kare rayukar dukkan jama’ar kasa ba tare da la’akari da kabilar su ko addini ko yankin da suka fito ba.

“Babba kuma muhimmin aiki da gwamnati zata yiwa jama’a shine kare rayukan su da dukiyoyin su. Haka tsarin yake ko ina a duniya, ba iya Najeriya ba kawai,” a cewar PDP

No comments:

Post a Comment