Thursday, 14 June 2018

Rasha ta lallasa Saudi Arabia da ci 5-0

Wasan farko da aka buga a gasar cin kofin Duniya a kasar Rasha tsakanin me masaukin baki kasar Rashar da Saudi Arabia ya kare Rashar na cin Saudi 5-0, da alama wannan gasar me tara kwallayece, Rasha sun nuna cewa ba za'a zo gidansu a fisu rawa da, dama masu iya magana na cewa duk wanda kaga an kada a gaban matarshi to iya karfinshi kenan.


A gobe ma akwai wasu wasannin wanda jama'a da dama ke son ganin yanda zata kaya, musamman tsakanin Spain da Portugal, sannan kuma akwai wasa tsakanin Egypt da Uruguay da kuma Morocco da Iran.

No comments:

Post a Comment