Thursday, 28 June 2018

Rawar da Ahmed Musa ya taka a gasar cin kofin Duniya tasa Leicester suka ce sun fasa sayar dashi ya zo yaci gaba da wasa

Rawar da tauraron dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya taka a gasar cin kofin Duniya da aka buga a kasar Rasha ta birge mutane sosai a ciki da wajen kasarnan, wani abu dake kara tabbatar da hakan shine yanzu kungiyarshi ta Leicester City da take shirin siyar dashi tace ta fasa sayar da Musan ya dawo ya ci gaba da wasa.


Leicester dai ta bayar da musa aro ga tsohuwar kungiyarshi ta CSKA Moscow kuma akwai rade-radin cewa zai bar kungiyar a kakarwasan da za'a shiga, amma yanzu kungiyar tace ta fasa sayar dashi yazo su zauna su tattauna yanda lamurra zasu kasance nan gaba, kamar yanda Owngoal suka ruwaito.

Kungiyoyin kwallon kafa biyar ne dai da suka hada da Benfica, da Olympique Marseille da Galatasary da Brighton da Hove Albion ke neman sayen Ahmed Musa din kamar yanda rahotanni suka bayyana.

No comments:

Post a Comment