Wednesday, 13 June 2018

Ronaldo Nazario yace Messi yafi birgeshi fiye da Ronaldo

Tsohon tauraron dan kwallon kafar kasar Brazil wanda kuma ya bugawa kungiyar Real Madrid wasa, Ronaldo Nazario ya bayyana cewa Messi yafi Cristiano Ronaldo buga wasa me kyau duk da cewa Ronaldon yana kokari sosai shima.


Ronaldo ya bayyana hakane a wata hira da akayi dashi a wani gidan talabijin na kasar Jamus me suna Sport Bild, da aka tambayeshi me zaice akan Cristiano Ronaldo?, sai yace yana kokari sosai musamman wajan ganin ya samu nasara a duk wasan da yake bugawa.

Amma maganar gaskiya Messi yafi bayar da gudummuwa a kwallo kuma yafi birgeshi, ya kara da cewa Messi ya iya wasa da kwallo a fili sosai kuma yana kai farmakin cin kwallo na bazata wanda ba kowane dan kwallone ke iya hakaba.

Amma yace Ronaldo zai iya samun nasara fiye da wadda ya samu a yanzu, inda yace cin kofin Duniya na da matukar muhimmanci ga dan wasan kwallo idan yana so ya shiga tarihin wadanda ba za'a manta da su ba. Yace amma lokacine dai kawai zai bayyana mana hakan.

Ronaldo Nazario dai ya lashe kofin Duniya har sau biyu lokacin da yayi tashen buga kwallonshi.

No comments:

Post a Comment