Wednesday, 20 June 2018

Ronaldo ya bayyana abinda ke bashi sa'ar cin kwallaye

A wasan da kasashen Morocco da Portugal suka buga a yau anga Cristiano Ronaldo da sabon gyaran fuska wanda ya dauki hankulan mutane sosai aka yi ta magana akanshi, Ronaldo ya bar dan gemu dan tsurut irin na awaki wanda kuma akwai wata kalmar turanci da ake gayawa wanda ya shahara wadda tayi kama da sunan akuya, watau GOAT, shine masoyan dan wasan suka rika bayyana cewa ya bar gemunne dan ya tabbatar da cewa shi na musammanne.


Abokin hamayyar Ronaldo, watau Messi tuni yana da irin wannan gemu kuma har a 'yan kwanakin baya kadan ya dauki hotuna da awaki da aka wallafa a mujallar PAPER wanda shima dan ya nuna cewa na musammane shi, wasu sun rika hada Ronaldon da cewa yana gasar gemunne da Messi.

A nashi bangaren da aka tambayeshi, Ronaldo yace suna wajan gyaran jikine sai ya gayawa Quaresma, cikin barkwanci cewa, bari in bar gemu irin na waki idan har naci kwallo a wasan mu na gaba to bazan askeshi ba har sai an kammala wannan gasar.

Ya kara da cewa, gashi kuma ya bani sa'a.

Ronaldo dai yaci kwallon kai a wasan da suka buga da kasar Morocco mintuna hudu da fara wasa.

Jayayyar waye na musamman ko kuna waye yafi wani na ci gaba da gudana musamman tsakanin masoyan 'yan wasan biyu.

No comments:

Post a Comment