Saturday, 16 June 2018

Ronaldo ya kafa tarihin kasancewa dan wasa mafi yawan shekaru da ya taba cin kwallaye uku a wasa daya a gasar cin kofin Duniya: Karanta yanda Ramos yayi hasashen cin kwallayen na Ronaldo tun kamin a buga wasan

A wasan da suka buga na jiya a gasar cin kofin Duniya, Kasashen Portugal da Spain sun tashi 3-3, abinda ya fi daukar hankulan mutane a wannan wasan shine kwallayen ukun da Cristiano Ronaldo yaci.


Tun kamin wannan wasan kusan kwanaki biyu da suka gabata, an tambayi Ramos ko tayaya zai tsayar da Ronaldo?, sai yace gaskiya be sani ba, abinda ma yake jin tsoro shine kar Ronaldon ya buga wasan da bai taba buga irinshiba a karawar tasu.

Hakan kuwa ta faru domin Ronaldo ya saka kwallaye uku a wasan, sannan kuma ya kafa tarihin kasancewa dan wasan kwallo mafi yawan shekaru daya ci kwallaye uku a wasa daya a gasar cin kofin Duniya. Shekarun Ronaldo di 33.

No comments:

Post a Comment