Tuesday, 19 June 2018

SAKO MAI MUHIMMANCI GA MASU HAWA MOTA DA DADDARE

Wannan sako ne daga group whatsapp dinmu na NIGERIA POLICE FORCE ana bada shawara ga wadanda suke tuka mota cewa da zaran kana tuka mota da daddare sai ka ga an jefo maka 'kwai na kaza (egg) a gaban gilashin motarka, to kada ka kuskura ka kunna abin share gilashin gaban mota (wiper), sannan kada ka watsa ruwa wa gilashin da zummar za ka goge koyin da aka jefo ya fashe maka a gaban gilashin mota.


Saboda shi koyin kaza yana haduwa da ruwa zai zama mai kauri kamar madara haka, don haka idan ka watsa wa koyin ruwa sannan ka kunna abin share gilashin gaban mota nan take zai dusashe maka hasken gilashin gaban motarka ta yanda ba zaka iya ganin gabanka tare da cigaba da tafiya ba, wanda daga karshe zai talista maka ka tsaya da tuki ka faka a gefe, to kana fakawa ka fada tarkon masu garkuwa da mutane.

Wannan shine sabon salon tarko da suka fito dashi domin su farauci al'umma.

A taimaka wajen yada wannan sakon domin jama'a su kubuta daga wannan sabon makirci na masu garkuwa da mutane

Allah muke roko Ya karemu gaba daya daga dukkan sharri da makirci da mugun tarko Amin.
rariya.

No comments:

Post a Comment