Wednesday, 13 June 2018

Sarkin Musulmi ya umarci Musulmai su nemi watan Shawwala daga Alhamis

Hukumar koli ta shariar Musulunci, NSCIA, dake karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ta umarci al’umma Musulmai dasu fita neman watan Shawwal, watan Sallah a ranar Alhamis, 14 ga watan Yuni, daidai 29 ga watan Ramadan.


Daily Trust ta ruwaito mataimakin babban sakataren mulki na hukumar, Farfesa Salisu Shehu ne ya bada sanarwar a ranar Talata, 12 ga watan Yuni, inda yace idan har mutanen kirki daga cikin Musulmai suka hangi watan, Sarkin Musulmi zai sanar da Juma’a a matsayin 1 ga watan Shawwal.

“Idan kuma ba’a hangi watan ba, ya zama kenan sallah zai kama ranar Asabar, 16 ga watan Yuni, 1 ga watan Shawwal kenan, don haka ake kira ga Musulmai dasu fita neman watan.” Inji Farfesan.

Mai alfarma Sultan ya taya Musulmai ganin karshen Azumin Ramadan, haka nan yayi adduar Allah ya amshi ayyukan ibadun da Musulmai suka yi a wannan watan.

Daga karshe sanarwar ta karkare da kira ga Musulmai da su fitar da zakkar fidda kai, wato zakkar kunu da nufin tallafa ma gajiyayyun cikinsu, sa’annan ta yi gargadi da kada a dinga karkatar da kayan abincin zuwa inda bai kamata ba.

No comments:

Post a Comment