Saturday, 2 June 2018

Sergio Ramos ya rera wa Spain sabuwar waka

Kaftin din Spain Sergio Ramos ya fitar da wata sabuwar waka da ya rera wa kasarsa domin gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha.


Dan wasan na Real Madrid ya fito a bidiyon wakar tare da mawakin Spain Demarco Flamenco.

Taken wakar shi ne 'Otra Estrella en tu Corazon' - ma'ana 'wata tauraruwa a zuciyarka'.

Ramos ya saki kadan daga cikin wakar a shafinsa na Instagram da za ku iya kallo a nan.
Baitikan wakar sun kunshi: "ku fito Spain ku daga murya da karfi ku kira kwallayen nan. Za mu cimma nasara idan muka sa kanmu, muka hada kai ga gwagwarmayar ganin La Roja ta kai ga nasara."

Bidiyon ya nuna Ramos da abokin wakarsa, kuma sama da mutane 82,000 suka kalli bidiyon jim kadan bayan sakinsa a ranar juma'a.

Ramos ya taba rera wa Spain waka mai taken 'La Roja Baila' a lokacin gasar cin kofin Turai a 2016.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment