Saturday, 9 June 2018

Shan ruwan Buhari da matasa: An zargi cewa miliyan biyu Buhari ya baiwa kowane matashi daya halarci gurin

A shekaran jiyane shugaban kasa, Muhammadu  Buhari ya gayyci matasan Najeriya fadarshi dake babban birnin tarayya, Abuja inda ya shirya musu liyafar shan ruwa wadda ta dauki hankulan 'yan Najeriya sosai.Saidai bayan da wannan lamari ya kare, wani bawan Allah yayi zargin cewa, wai kowane matashi daya halarci gurin shan ruwan, shugaba Buhari ya bashi miliyan biyu, ya kara da cewa yanzunan zakaji matasan sun fara yiwa Buharin yakin neman zabe. Ya karke labarinshi da barkwanci inda yace, kai akwai Yunwa.

Saidai me baiwa shugaban kasar shawara akan sabbin kafafen sadarwa, Bashir Ahmad ya mayarwa da mutumin martani cikin gatse da cewa, Baka ji ba da kyau, miliyan ashirinne aka baiwa kowane matashi, ka sake tambayar wanda ya baka labarin.

Lamarindai ya dauki hankula inda wasu daga cikin wanda suka halarci wancan shan ruwa suka fito suka karyata wannan batu.

No comments:

Post a Comment