Monday, 11 June 2018

Shima yasan karya yake min>>Guardiola ya mayarwa da Yaya Toure martani

A makon daya gabatane tauraron dan kwallo, Yaya Toure ya bayyana cewa kocin Man City, Pep Guardiola na nunawa 'yan wasan da suka fito daga yankin Afrika wariyar launin fata, da farko da aka tambayi kungiyar Man Cityn da kocin duk sunki cewa uffan akan wannan lamari amma yanzu Guardiola yace Yaya Toure karya yake masa.


A wata hira da akayi dashi a wani gidan talbaijin, Guardiola yace, Yaya Toure karya yake mishi, shima kuma yasan da haka.

Ya kara da cewa, Shekarar su biyu suna tare, me yasa be taba gayamishi hakan ba gaba- da- gaba.

Saidai ya kuma yabi Toure din inda yace kwararren dan kwallone wanda ya kamata ace yana buga wasa a kungiyoyin da suka sharara irin su Arsenal, Chelsea, Liverpool da sauransu.

No comments:

Post a Comment