Saturday, 9 June 2018

Shugaba Buhari ya sakawa dokar data hana mataimakan shuwagabanni yin wa'adin mulki sama da daya bayan sun gaji kurar

Me baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin majalisa, Ita Enang ya bayyanawa manema labarai cewa shugaban kasar ya saka wa dokar da ta baiwa mataimakin shugaban kasa da mataimakin gwamna karin wa'adi daya idan ya zamanto cewa sun gaji shugabansu.


Enang ya bayyana cewa idan shugaban kasa ko gwamna ya mutu ko kuma aka tsigeshi ko ya ajiye aiki mataimakinshine doka ta baiwa damar hawa kujerar, dan haka za'a rantsar dashi a matsayin shugaban kasa.I dan haka ta faru to sabuwar dokar da shugaba Buhari ya sakawa hannu tana cewa wa'adi daya mataimakin zai iya karawa a kan mulki ya sauka.


No comments:

Post a Comment