Saturday, 30 June 2018

Shugaba Buhari ya tafi kasar Mauritania halartar taron kungiyar kasashen Afrika

Da safiyar yau, Asabar, shugaban kasa, Muhammadu Buhari tare da masu mai rakiya, gwamnonin, Nasarawa, Tanko Almakura dana Edo, Godwin Obaseki da wasu manyan jami'an gwamnati sun tafi kasar Mauritania.
Shugaba Buharin zai halarci taron kungiyar kasashen Afrikane da za'ayi a can haka kuma zai gana da wasu shuwagabannin kasashen Afrika akan dangantakarsu da Najeriya. Zai kuma kasance cikin shuwagabannin da zasu gana da shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron.


Muna fatan Allah ya kaisu lafiya ya dawo dasu lafiya.

No comments:

Post a Comment