Sunday, 10 June 2018

Shugaba Buhari ya tafi kasar Morocco

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tafi kasar Morocco a yau, Lahadi inda zai shafe kwanaki biyu yana ziyara acan, a jiyane fadar shugaban kasar ta bayyana cewa shugaba Buharin da Sarki Muhammad VI na Moroccon zasu tattauna dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma ci gabansu.


Muna fatan Allah ya kaishi lafiya ya kuma dawo dashi lafiya.
No comments:

Post a Comment