Thursday, 14 June 2018

Shugaba Buhari yayi bankwana da jakadun kasashen Turkiyya da Ethiopia da suka gama aikin jakadancinsu a Najeriya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi bankwana da jakadun kasashen Ethiopia, Samina Zekaria Gutu da kuma na kasar Turkiyya, Hakan Cakil yayin da suke kammala ayyukansu na jakadanci a Najeriya.


Shugaba Buhari ya gana da jakadun biyu a fadarshi, yau, Alhamis inda ya musu fatan Alheri a ayyukan su da zasu kama nan gaba da kuma jaddada huddar diplomasiyya tsakanin kasashensu da Najeriya.
No comments:

Post a Comment